KanoOnline Online Forum KanoOnline Online Forum
February 07, 2012, 04:50:02 PM *

Login with username, password and session length
News: Please check your user profile to make sure you have the correct e-mail address. Thanks...
 
   Home   Help Search Calendar Articles Downloads Gallery Login Register  
Pages: [1] 2   Go Down
  Print  
Author Topic: Wasan Hausa Ya Sabama Hankali  (Read 13690 times)
0 Members and 1 Guest are viewing this topic.
Sirajo Ibrahim
Member
*
Offline Offline

Location: Gusau, Zamfara
Posts: 9

View Profile Awards
« on: June 08, 2005, 08:51:07 PM »

'Yan wasan Hausa Na wannan karni sufara kaucewa dokoki da kaido jin wansan hausa Mu sammamma Al'adum Hausawa, Yaza a yi a ciyo kansu
a kuma dorasu su daidaitu kan al Adummu na hausawa?
Logged

oriki
salizone
Member
*
Offline Offline

Location: Zaria
Posts: 4

View Profile Awards
« Reply #1 on: June 11, 2005, 07:08:15 PM »

Gaskiyar ka, amma ni yadda na dauka lokaci ne, kuma zai wuce da sannu za a zo lokacin da za su canja su koma yin irin wanda kake ganin shine daidai, don da haka ci gaban wasan kwaikwayo ke farawa a ko ina.
Ina nufin yana farawa ne daga kwaikwayon wasu.
Logged
mlbash
Super Member
*****
Offline Offline

Location: kano
Posts: 806

View Profile Awards
« Reply #2 on: June 16, 2005, 11:25:26 AM »

Quote from: "salizone"
Gaskiyar ka, amma ni yadda na dauka lokaci ne, kuma zai wuce da sannu za a zo lokacin da za su canja su koma yin irin wanda kake ganin shine daidai, don da haka ci gaban wasan kwaikwayo ke farawa a ko ina.
Ina nufin yana farawa ne daga kwaikwayon wasu.

 gaskiya ban yarda da kai ba. domin kuwa daga yadda take taken su yake gamai hankali da hangen nesa, wallahi kiris suke jira su fada ramin kura! ina fata ka gane inda na nufa. ina ganin lailai ne gwamnati ta kara dagewa ka kula da tsarin hausa fim kafin lokaci ya kure mana. domin kuwa idan mu mun tsira, tofa kannanmu da 'ya'yenmu na tasowa!
 ALLAH ya shirye mu.
Logged

t is my intention to make the neglected aspect of our societies viable
salehjnr
Member
*
Offline Offline

Location: Maiduguri
Posts: 1

View Profile Awards
« Reply #3 on: February 23, 2006, 02:33:29 PM »

A gaskiya dai a duba a gani domin yadda abubuwa suke kasancewa game da yana yin fina-finan hausa abin sai dai addu`a kuma gaskiya batun wai zasu daina (lokaci ne) bai ma taso ba, domin in aka yi la`akari da yadda indiyawa suka soma to za ka tarar cewa lallai in ba an dauki matakai ba to lallai wataran za muyi da na sani, domin tarihi ya nuna cewa farkon fara fina-finan indiya, kusan ba a samun mace ta zama jarima, sai dai ayi wa namiji kwalliyar mata ya rika acting kamar mace saboda tsabar al`ada da kunya irin tasu amma sannu a hankali sai gashi yau indiyan fim ya zama tamkar fin din America. saboda haka muyi hattara, domin hausawa sun ce tafi dai Guga................
Logged
mlbash
Super Member
*****
Offline Offline

Location: kano
Posts: 806

View Profile Awards
« Reply #4 on: March 03, 2006, 11:46:19 AM »

duba min hanya abokina!
Logged

t is my intention to make the neglected aspect of our societies viable
nuramagaji
Member
*
Offline Offline

Location: no 25 gorondutse kano nigeria
Posts: 9

View Profile Awards
« Reply #5 on: June 16, 2006, 09:16:44 PM »

kafin kurinka fadin irin wadannan kalmomi yakamata ku shiga cikin masu wannan wasanni kuyi nazari :twisted:
Logged

ello for every body
jaybee
Member
*
Offline Offline

Posts: 10

View Profile Awards
« Reply #6 on: March 13, 2007, 09:38:15 AM »

Assalam Alaikum!
Ni a gani na komai na bukatar lokaci, domin kuwa idan ka yi la'akari da samuwar fina-finan Hausa za ka ga abin jariri ne, idan ka kwatanta shi da suaran wasu abubuwa na Adabi. Kuma shawara a nan ina ganin ya kamata a shiga wannan harka ta fina-finai a santa ciki da waje, sannan a gano inda ta yi gibi, to unsha allahu wata rana za su dace da rayuwar Hausawa.
Ma'assalam.
Logged
HUSNAA
Super Member
*****
Offline Offline

Gender: Female
Location: In Limbo
Posts: 2896

Life's but the blink of an eye:spend it gratefully

View Profile Awards
« Reply #7 on: March 14, 2007, 01:24:07 PM »

Jama'a jinku nake kurum ko kuwa karanta ku nake kurum. Ina ga wa'yanda suke cewa ayi hattara in ba hakaba al'a dun mu na hausa za su bace? Abin da nake so in janyo hankalin marubuta shine, abin da 'yan wasan kwaikwayo ke yi ba wani abu bane illa kwaikwayar yadda zamani ya kasan ce. Duk abinda suke nuna wa abin da ake aikatawane a yanzu. Ba su suke canza al'adar Hausawaba, kuma ba su za su can za taba. Abin da suke gani a nayi a cikin alumma shi su ke kwaikwaya suna fito da shi fili. Shi yasa a ke kiran su 'yan wasan kwaikwayo.
Misali, yawanci ana sukar 'yammatan wasan kwaikwayo da rashin saka kayan da muka gada a aladance. Watau suna sa kananan kaya- dogon wando da t shirt ko makaman tansu. Yanzu ina ce duk yara yaran 'yammatan yanzu ba haka suke dressing ba? In ka ga yarinya ba tayi ba, to batada halin yi ne, kokuwa gidan su a tsakiyar cikin birni Kano yake inda baza ta samin sukunin yin haka ta fita ba. Amma ba abin da ke hana ta a cikin gidan iyayen ta. Kuma sanin kowa ne cewa su 'yammantan masu yin wasan kwaikwayon basu su ka fito da al'adar sa kananan kaya ba. Do min na san cewa a wani lokacin ma, in sun tafi yin film musamman ma in a gidajen mutane ne (watau private residence) har aron kayan sawa ake basu don suyi fim din. Ni wannan na gani da ido na.

Na biyu kuma duk akan kaya. Yanzu yan mata nawa ne ke lullubi in za su fita? Ba wani dan karamin gyale ake yafawa a ka ba yana yi yana zame wa yana nuna adon gashin yarinya ita kuma ta na dan karkata shi wai ita tana gyara lullubi? 'Yan wasan Hausa ne suka bullo de wannan yayin? Ina Stella Obasanjo? Style din riguna da sukayi tashe a 'yan shekarun da suka shige. Tabbas ana ganin 'yan wasan kwaikwayo suna sa irin wannan sitturar amma ba su suka kirkiro da style din stella obasanjo ba.
In kuma ana batun soyayya fa? E to, ba a ganin mace da namiji suna rawa kamar yadda ake nunawa a fim din Hausa, amma kuma ko ni nan lokacin ina daliba a BUK, naje irin liyafar nan da ke shiryawa watau night parties. A wurin akwai mata da maza a hade. Kuma anayin raye rayen disco da makaman tan su. Saboda haka ba'a ce wai 'yan wasan kwaikwayo ne za su canza mana al'adu ba. Sun riga sun fara canzawa, tun shekaru aru aru.

Bayan da haka da mu Hausawa bamu nuna matukar mugun sha'awar finafinan Indiya ba, su 'yan wasan hausan baza su kwaikwaye su har mu kuma muzo muna korafi wai za a canza mana aladu. In mun san abinda 'yan fim din Indian suke yi bashi da kyau, me yasa muka rika kallon finafinan nasu? Har dan azabar lakance indian films wa'yansu ma  da basu taba zuwa India  ba sun fahimci harshen Hindi abakin su kamar jakunan Calcutta ko Mumbai  Grin.
Dan Allah a ruka sara a na duban bakin gatari. Ba ruwan 'yan finafinan hausa da gurbata al adun Hausawa, Kwaikwayo kurum suke yi kamar yadda lakanin nasu yake.
« Last Edit: March 14, 2007, 01:31:41 PM by HUSNAA » Logged

Ghafurallahi lana wa lakum
Dan-Borno
Super Member
*****
Offline Offline

Gender: Male
Location: Maiduguri
Posts: 2379

EVERYTHING HAPPENS FOR A REASON

View Profile WWW Awards
« Reply #8 on: March 14, 2007, 03:25:54 PM »

Lallai kuwa Babbar Malama ta gama zancen gaba
daya a dunkule.

Abin da zamu ce shine, kowa ya fara gyara daga
kansa da iyalinsa.
Logged

"My mama always used to tell me: 'If you can't find somethin' to live for, you best find somethin' to die for" - Tupak
jaybee
Member
*
Offline Offline

Posts: 10

View Profile Awards
« Reply #9 on: March 16, 2007, 05:05:38 PM »

Assalamu Alaikum,

A gaskiya na ji dadin bayaninki  HUSNAA kwarai da gaske, Allah ya saka da alheri, Allah kuma ya sa 'yan uwa su gane.Domin kuwa abin da kika fada gaskiua ne, ba 'yan wasan Hausa ba ne suke bata tarbiyyar 'ya'yan Hausawa ba, su dai suna nuni da irin abubuwan da suke faruwa ne a zamani, domin a yi hattara

Ashe daman akwai JAKIN MUMBAI Grin, wallahi ban taba ji ba sai a wajenenki
Ma'assalam
Logged
Fateez
Super Member
*****
Offline Offline

Gender: Female
Posts: 597

View Profile Awards
« Reply #10 on: March 18, 2007, 09:06:03 AM »

Misali, yawanci ana sukar 'yammatan wasan kwaikwayo da rashin saka kayan da muka gada a aladance. Watau suna sa kananan kaya- dogon wando da t shirt ko makaman tansu. Yanzu ina ce duk yara yaran 'yammatan yanzu ba haka suke dressing ba? In ka ga yarinya ba tayi ba, to batada halin yi ne, kokuwa gidan su a tsakiyar cikin birni Kano yake inda baza ta samin sukunin yin haka ta fita ba. Amma ba abin da ke hana ta a cikin gidan iyayen ta. Kuma sanin kowa ne cewa su 'yammantan masu yin wasan kwaikwayon basu su ka fito da al'adar sa kananan kaya ba. Do min na san cewa a wani lokacin ma, in sun tafi yin film musamman ma in a gidajen mutane ne (watau private residence) har aron kayan sawa ake basu don suyi fim din. Ni wannan na gani da ido na.

Na biyu kuma duk akan kaya. Yanzu yan mata nawa ne ke lullubi in za su fita? Ba wani dan karamin gyale ake yafawa a ka ba yana yi yana zame wa yana nuna adon gashin yarinya ita kuma ta na dan karkata shi wai ita tana gyara lullubi? 'Yan wasan Hausa ne suka bullo de wannan yayin? Ina Stella Obasanjo? Style din riguna da sukayi tashe a 'yan shekarun da suka shige. Tabbas ana ganin 'yan wasan kwaikwayo suna sa irin wannan sitturar amma ba su suka kirkiro da style din stella obasanjo ba.

Wallahi kin fadi gaskiya. Yan wassan hausa kawai reflecting abin da

ke faruwa a society suke yi. Ba ruwansu da kikiro abubuwan da ake

laka masu. Kuma mutanen da suke zagin yan film idan an bincika irin

abubuwan da suke yi ya fi haka baci ma...

Allah dai ya shirya gabaki daya.
Logged

"The only way of finding the limits of the possible is by going beyond them into the impossible." ~ Arthur C. Clarke
bakangizo
Super Member
*****
Offline Offline

Location: Kano
Posts: 1871

View Profile Awards
« Reply #11 on: July 19, 2007, 05:05:11 PM »

Jama'a jinku nake kurum ko kuwa karanta ku nake kurum. Ina ga wa'yanda suke cewa ayi hattara in ba hakaba al'a dun mu na hausa za su bace? Abin da nake so in janyo hankalin marubuta shine, abin da 'yan wasan kwaikwayo ke yi ba wani abu bane illa kwaikwayar yadda zamani ya kasan ce. Duk abinda suke nuna wa abin da ake aikatawane a yanzu. Ba su suke canza al'adar Hausawaba, kuma ba su za su can za taba. Abin da suke gani a nayi a cikin alumma shi su ke kwaikwaya suna fito da shi fili. Shi yasa a ke kiran su 'yan wasan kwaikwayo.
Misali, yawanci ana sukar 'yammatan wasan kwaikwayo da rashin saka kayan da muka gada a aladance. Watau suna sa kananan kaya- dogon wando da t shirt ko makaman tansu. Yanzu ina ce duk yara yaran 'yammatan yanzu ba haka suke dressing ba? In ka ga yarinya ba tayi ba, to batada halin yi ne, kokuwa gidan su a tsakiyar cikin birni Kano yake inda baza ta samin sukunin yin haka ta fita ba. Amma ba abin da ke hana ta a cikin gidan iyayen ta. Kuma sanin kowa ne cewa su 'yammantan masu yin wasan kwaikwayon basu su ka fito da al'adar sa kananan kaya ba. Do min na san cewa a wani lokacin ma, in sun tafi yin film musamman ma in a gidajen mutane ne (watau private residence) har aron kayan sawa ake basu don suyi fim din. Ni wannan na gani da ido na.

Na biyu kuma duk akan kaya. Yanzu yan mata nawa ne ke lullubi in za su fita? Ba wani dan karamin gyale ake yafawa a ka ba yana yi yana zame wa yana nuna adon gashin yarinya ita kuma ta na dan karkata shi wai ita tana gyara lullubi? 'Yan wasan Hausa ne suka bullo de wannan yayin? Ina Stella Obasanjo? Style din riguna da sukayi tashe a 'yan shekarun da suka shige. Tabbas ana ganin 'yan wasan kwaikwayo suna sa irin wannan sitturar amma ba su suka kirkiro da style din stella obasanjo ba.
In kuma ana batun soyayya fa? E to, ba a ganin mace da namiji suna rawa kamar yadda ake nunawa a fim din Hausa, amma kuma ko ni nan lokacin ina daliba a BUK, naje irin liyafar nan da ke shiryawa watau night parties. A wurin akwai mata da maza a hade. Kuma anayin raye rayen disco da makaman tan su. Saboda haka ba'a ce wai 'yan wasan kwaikwayo ne za su canza mana al'adu ba. Sun riga sun fara canzawa, tun shekaru aru aru.

Bayan da haka da mu Hausawa bamu nuna matukar mugun sha'awar finafinan Indiya ba, su 'yan wasan hausan baza su kwaikwaye su har mu kuma muzo muna korafi wai za a canza mana aladu. In mun san abinda 'yan fim din Indian suke yi bashi da kyau, me yasa muka rika kallon finafinan nasu? Har dan azabar lakance indian films wa'yansu ma  da basu taba zuwa India  ba sun fahimci harshen Hindi abakin su kamar jakunan Calcutta ko Mumbai  Grin.
Dan Allah a ruka sara a na duban bakin gatari. Ba ruwan 'yan finafinan hausa da gurbata al adun Hausawa, Kwaikwayo kurum suke yi kamar yadda lakanin nasu yake.
Kai, amma naji dadin wannan bayani naki. Wallahi a duk lokacin da nake kokarin kare 'yan fim a kan zargin suna bata al'adar hausa ina kawo wasu dalilai irin nawa, amma ban taba tunanin wannan ba. Ni dai abin da na sani shine dama can al'adar mu ta dauko lalacewa tun gabannin fara wasannin hausa. Kuma in ma ance a daina kallon wasan hausa, ai dai yawancin mutane yanzu suna da satelites  a gidajen su. To ana nufin kallon American films da Indian Films da Nollywood yafi alheri, tun da dai ba za'a iya hana mutane kallon film ba gaba daya?

Na yarda akwai gyare-gyare a harkar fim din hausa, kuma ya kamata a dau matakin gyara, amma cewar su ke bata al'adar mu ba'a yi musu adalci ba.
« Last Edit: July 19, 2007, 05:13:00 PM by Bakan~Gizo » Logged
amira
Super Member
*****
Offline Offline

Gender: Female
Location: an island
Posts: 848

View Profile Awards
« Reply #12 on: July 20, 2007, 03:41:29 PM »

Ai dama husnaa ta iya bayani da bada amsa mai kyau. Wink
Logged

*Each day is definately defining me and finding me*
HUSNAA
Super Member
*****
Offline Offline

Gender: Female
Location: In Limbo
Posts: 2896

Life's but the blink of an eye:spend it gratefully

View Profile Awards
« Reply #13 on: July 21, 2007, 10:48:49 AM »

 Amira u r 2 kind........thanks for the flattering comment Grin Grin Grin
Logged

Ghafurallahi lana wa lakum
amira
Super Member
*****
Offline Offline

Gender: Female
Location: an island
Posts: 848

View Profile Awards
« Reply #14 on: July 23, 2007, 04:19:37 PM »

to ai gaskiya ne malama husnaa Cheesy
Logged

*Each day is definately defining me and finding me*
Pages: [1] 2   Go Up
  Print  
 
Jump to:  

Subject Started by Replies Views Last post
Biography Of A Fulani Slave In America Dan Yusuf 1 4934 Last post April 29, 2005, 08:08:28 AM
by Anonymous
DISCOURSE ON MODERNITY, AN INTELLECTUAL TRIVIALITY _Waziri_ 8 2356 Last post May 24, 2004, 05:03:27 PM
by _Waziri_
Lugard's Dual Mandate and Leadership Experiment JiboNura 0 1456 Last post January 12, 2004, 12:28:57 PM
by JiboNura
Failure of Nigerian State: Re-Drawing The Fault Lines _Waziri_ 12 3092 Last post February 23, 2005, 09:58:54 AM
by _Waziri_
Balewa "Died of Asthma Attack", not Killed by Soldiers - Mbu maxsiollun 6 1405 Last post October 15, 2010, 02:29:19 PM
by gogannaka
Powered by EzPortal
Powered by SMF 1.1.15 | SMF © 2011, Simple Machines
Page created in 1.484 seconds with 28 queries.